Ana bata mana suna — Malaman Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Malamai da Limamai sun yi taro a Kaduna domin duba yadda al'amurra ke gudana a Najeriya.

A Najeriya, wasu Malaman addinin Musulunci sun koka akan halayyar wasu daga cikin su da ke zubar musu da kima a idon jama'a.

Malaman sun kuma nuna damuwa game da yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da Malamai a lokutan yakin neman zabe amma da zarar an yi zabe kuma su juya musu baya.

Malaman-- karkashin Majalisar Malamai da Limamai ta jihar Kaduna -- sun bayyana haka ne a wani taro da suka gudanar domin duba yadda al'amura ke gudana a Najeriya.

Sun kuma bayyana takaicin su game da yadda wasu Malamai suka koma tamkar dillalai na 'yan siyasa domin zawarcin wasu Malamai wadanda daga bisani kuma su yi watsi da su bayan cimma burin su.