Mayakan IS sun tarwatsa ginin Bel a Syriya

Image caption Daya daga cikin gine-ginen tarihi a Palmyra

Rahotanni daga Syria sun ce mayakan kungiyar IS sun lalata wasu bangarori na wani tsohon ginin tarihi da ake yin bauta a ciki a birnin Palmyra.

Ginin da ake kira wurin Bauta na Bel, yana daga cikin manyan wurare masu dinbin tarihi da ake da su a duniya.

Kungiyar kare hakkin dan adam a Syria mai hedikwata a Burtaniya ta ce mayakan kungiyar IS sun yi amfani da bama bamai masu yawa wajen tarwatsa sassan ginin tarihin na Bel.

A cikin makon jiya, kungiyar IS ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda mayakanta suka lalata wani katafaren ginin Baalshamin da aka gina shekaru 2000 a birnin nan Palmyra.

Hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana barnar da aka yi a gine ginen a matsayin wani laifi na yaki.