Zanga zanga akan muzgunawa baki a Austria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga sun yi addu'o'i ga wadanda suka mutu a cocin Saint Stephen's Cathedral.

Dubban mutane sun ba zu akan tituna a Vienna, babban birnin kasar Austria inda suke zanga-zanga akan muzgunawa 'yan gudun hijira.

Galibin masu zanga zangar sun rike kwalaye dauke da rubuce rubuce da ke cewa; "Maraba 'yan gudun Hijira" da kuma "Bama son nahiyar turai ta koma wurin binne tarin gawarwaki".

A makon jiya ne aka gano gawarwakin 'yan cirani 71 a wata motar daukar kaya da aka aje a gefen babban titi da ake kyautata zaton sun fito ne daga Syria.

Masu zanga-zangan sun kuma yi jerin gwano inda aka gudanar da addu'o'i ga wadanda suka mutu a cocin Saint Stephen's Cathedral.

Kasar Austria ta kara tsaurara binciken motocin dake shigowa kasar daga Hungary don duba 'yan cirani, inda jami'an 'yan sanda suka ce kimanin 'yan gudun hijira dubu daya ne suka iso babbar tashar jirgin kasa dake Vienna daga Budapest a ranar juma'a, inda da dama daga cikin su suka shiga jirgi zuwa kasar Jamus.