Marina a Kano sun sasanta da 'yan China

Image caption Matasa masu sana'ar rini a yayin zanga-zangarsu kan 'yan China. Matsalar da yanzu aka warware ta hanyar yarjejeniya da su da kuma gwammnatin jihar Kano

An sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin kungiyar masu rini a Kano, da cibiyar ciniki da masana'antu ta kasar China, da kuma gwamnatin jihar Kano, wacce ta hana 'yan China kawo runannun kaya jihar ta Kano.

Yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa masu rinin za su riga sayen kayayyakin da suke amfani da su yayin rinin daga wajen 'yan China.

Za kuma su rika saye ne a jimlace ba a karkashin kungiyarsu ta 'yan rini ba da cinikin dai-dai ba.

Wannan mataki dai ya biyo bayan korafe-korafen da masu rinin suka yi cewa runannun tufafin da 'yan Chinan ke kawo wa suna kashe musu kasuwa, inda suka mai da dubban matasa marasa ayyukan yi.