'Yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption 'Yan gudun hijira da dama na cikin matsanancin hali a Najeriya da Kamaru

Kungiyar jin kai ta "Red Cross" ko "Croix rouge", ta koka kan halin da wasu 'yan Kamaru kimanin 8,000 ke ciki sakamakon tserewar da suka yi daga matsuguninsu i zuwa birnin Kousseri domin neman mafaka.

Mutanen sun samu kansu a cikin wannan halin ne sanadiyar farmakin da kungiyar Boko Haram take kai wa a wasu sassan Kamaru kusa da gidajensu.

Kungiyar ta ce wadannan mutane na bukatar taimakon abinci da kuma samun muhalli.

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi ya yi sanadiyar raba dubban mutane da muhallansu.