Sojin Nigeria sun kwato Gamboru Ngala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Najeriya na ci gaba da kokarin murkushe ayyukan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta kwace ikon garin Gamboru Ngala, da ke jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram a ranar Talata.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya ce yanzu haka dakarun suna ta kokarin tattaro kayan aikinsu da kuma motocin sintiri.

Dakarun sojin Najeriyar na cikin murnar wannan galaba da suka samu a kan Boko Haram.

A baya sojojin Chadi sun karbo garin a hannun 'yan Boko Haram, amma daga bisani kuma suka sake karbe wa.