Paparoma zai yi afuwa ga masu zubda ciki

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Paparoma FRancis zai yi afuwa ga masu zubda ciki

Paparoma Francis zai bai wa limaman babban cocin Katolika, zabin yafewa matan da suka zubar da ciki.

Fadar Vatican ta wallafa wata wasika wadda a cikinta Paparoma Francis ya kwatanta matsalar ta matan da suka zubar da ciki ke fuskanta.

Ya ce ya hadu da mata da dama da ke neman afuwa wadanda a cikin zuciya suke tsananin da na sanin matakin da suka dauka.

Kafin yanzu dai zubar da ciki wani babban laifi ne a koyarwar Katolika kuma wadanda suka aikata na zama saniyar ware.