Amurka za ta tallafawa 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan gudun hijira da ke sansanin Yola

Amurka ta sanar da bayar da tallafin dala 801,000 ga 'yan gudun hijirar da ke neman mafaka a Jimeta da Yola na jihar Adamawa.

Wata jami'ar hukumar bayar da agaji ta Amurka USAID Maria Brewer, ta ce tallafin zai taimaka wajen inganta harkokin ilimi ga daukacin 'yan gudun hijirar.

Daraktan hukumar Michael T. Harvey, ya sanya hannu kan yarjejeniyar da jami'ar Amurka a Najeriya wato ABTI American University, a gaban wasu jami'an ofishin jakadancin Amurka da manyan malaman jami'o'i na Najeriya.

Zuwa yanzu dai adadin tallafin jin kai da Amurka ta bai wa jami'ar tun daga fara rikice-rikicen kungiyar Boko Haram a yankin ya kai $901,000.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a arewacin Nigeria.