Lantarki ya kashe mutane 4 a Arugungu

Hakkin mallakar hoto kebbi government
Image caption Gwamman Jihar Kebbi Atiku Bagudu

Rahotannin daga garin Argungu na jihar Kebbi na cewa a kalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar fashewar na'urar rarraba wutar lantarki wato Transformer.

Hatsarin ya faru ne a lokacin da wata na'urar ta yi bindiga kuma ta kama da wuta a daren Laraba.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, a sakamakon tserewa daga wurin ne mutanen hudu suka hallaka, yayin da shida kuma suka jikkata.

Rahotanni sun ce har yanzu mutanen unguwar da al'amarin ya faru suna cikin rudani tare da alhini.