Ana zaman dar-dar a Bujumbura

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane sun bazama kan tituna saboda aniyar shugaba Nkurunziza

An wayi gari a Bujumbura, babban birnin Burundi da jin karar harbe-harbe, musamman ma a yankunan da masu adawa da gwamnatin shugaba Nkurunziza suka yi kaka-gida.

Rahotanni dai na cewa a kalla mutum biyu sun mutu, kuma jama'a na ta ficewa daga kasar zuwa kasashe makwabta.

Wani ofishin majalisar dinkin duniya da ke Tanzania, ya ce a kowace rana sama da 'yan gudun-hijira 400 ne daga kasar Burundi ke shiga Tanzania.

Wannan lamari dai na faruwa ne kusan makonni uku bayan shugaba Pierre Nkurunziza ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama.

An dade ana fama da rikici a kasar Burundi sakamakon rashin jituwa tsakanin masu neman mukaman siyasa.