Motorola ya kirkiro agogon Moto 360

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Farashin zai fara ne daga £229 idan aka fara sayar da agogon nan gaba a watan Satumba.

Kamfanin Motorola ya sanar da fitar da sabbin agogonan komai da ruwanka na zamani mai suna Moto 360 dauke da manhajjar Android.

Agogonan za su kasance kala biyu inda na farko aka sanya na'urar GPS don gano wurare a duk lokacin da ba'a hada agogon da wayar tarho ba.

Kamfanin ya ce za a ba masu sha'awar agogon damar zana irin yadda suke son fasalin agogon su a duk lokacin da suka yi odar agogon daga kamfani.

Motorola ya fitar da sabbin agogunan ne a kasuwar baje kolin kayayyakin fasaha a Berlin.

Farashin kowane agogo ya danganta daga irin kirar sa, amma farashin zai fara ne daga £229 idan aka fara sayar da agogonan nan gaba a watan Satumba.