'Mulki a Nigeria ba tare da ministoci ba'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A cikin shirin BBC na jerin wasikun 'yan jarida na kasashen Afrika, Mannir Dan Ali ya yi dubi kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati a Nigeria ba tare da an nada ministoci ba.

Watani uku kenan tun bayan da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Nigeria kuma watanni biyar tun bayan da ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi mai tarihi, inda a karon farko da dan takara na jam'iyyar adawa ya yi nasara.

'Yan Nigeria da dama sun yi murna sosai a kan nasarar da ya samu kuma sun rika fatan cewa hakan zai bude wani sabon babi a tarihin kasar, inda wasu suka rika tsammanin cewa manyan sauye -sauye za su biyo baya, yayinda masu sharhi suka bukaci sabon shugaban kasar a kan ka da ya bata lokaci wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa.

Galibin 'yan Nigeria sun sa ran cewar shugaba Buhari zai yi wa hafsoshin sojin kasar garanbawul tare da aiwatar da wasu muhimman nade-nade a farkon kwanakinsa kan mulki kamar yadda tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo ya yi bayan 'yan sa'o'i da aka rantsar da shi a matsayin shugaban Nigeria a zamanin mulkinsa..

Sai dai shugaba Buhari ya dauki kusan watanni biyu kafin ya nada sabbin hafsohin tsaro na kasar kuma ya nada mutane a mukamai kusan goma sha biyu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu alhakin kawar da Boko Haram

A yanzu an samu sabbin hafsoshin soji da aka dorawa alhakin murkushe mayakan kungiyar Boko Haram.

Haka kuma a lokacin da masu sharhi kan lamura suka soma magana a kan rashin kafa majalisar ministoci, wani tsohon edita kuma na hannun damansa ya rubuta wani labari mai taken "shin wai mai ya janyo gunaguni"?

Ya yi kira ga 'yan jarida da masu amfani da shafukan sada zumunta da sauransu a kan su mai da hankali a kan "makiyan Nigeria na asali watau talauci da fatara da jahilci da cututtuka da kuma almabazaranci" kuma ya ce bai kamata su kasance wadanda za su hana ruwa gudu ba ga shugaban kasa mai farin jini a Nigeria.

"Sabuwar gwamnatin ta hau mulki ne ta hanyar ikon da mutane suka bata, a kan haka nauyi ya rataya a kanta wajen ganin ta tsara tare da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar mutane ba tare da nuna damuwa ba a kan wane mukami ne za a ba wasu ba," in ji marubucin.

Duk da cewa marubucin ya fadi gaskiya a wasu wurare amma sabuwar dimokradiyar kasar ta sa ya kasance abu mai wuya a samu mutane da dama da za su rika sukar shugaba Muhammadu Buhari a bainar jama'a.

'Tabarbarewar al'amura'

An samu wata majiya daga can kololuwa da ta ce sai a watan Satumba ne za a kafa majalisar ministoci.

A cewar majiyar hakan ya biyo bayan kasancewa kusan abubuwa da dama na kasar sun tababbare.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yan Najeriya na son ganin canji a kasa

Magoya bayan Muhammadu Buhari na fatan zai kawo sauyi a cikin kasar.

"Ba bu yadda za a yi sabuwar gwamantin ta cimma muradunta ba tare da ta shinfida sabon tubali ba."

Hakan ya biyo bayan labarin da jaridar Washington Post ta buga inda shugaba Buhari ya bayyana ra'ayinsa a dai-dai lokacin da ya kai ziyara Amurka a watan daya gabata, inda ya yi karin haske a kan dalilan da suka sa ba zai yi hanzari ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ba."

"Sai dai ya kamata a ayi la'akari da cewa ko shi kansa shugaban Obama sai da ya shafe tsawon watanni a kan karagar mulki kafin ya nada mukamai kuma duk da haka al'amura ba su tsaya cik ba," in ji Buhari.

A Nigeria kuwa abu ne da ba zai yi tasiri ba ko ya sa gwamnati ta cimma burinta idan ta nada mutane da za su rike mukaman siyasa ba tare da bata lokaci ba, bayan hawanta kan karagar mulki, a kan haka ya zaman dole ne ga Najeriya ta soma aiwatar da sabbin sharudda na kyakyauwan shugabanci .