Malaman Firamare a Filato na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto nigeria lalong
Image caption Gwamna Lalong ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalar daga gwamnatin Jang

Rahotanni daga jihar Filato a Nigeria na cewa malaman makarantun Firamare masu koyar da darusan addinin kirista da musulunci na cikin wani mawuyacin hali saboda rashin biyansu albashi na watannin goma sha takwas.

Wani malamin makarantar ta Firamere ya yi wa BBC karin bayani cewa "Wallahi yanzu watanmu 18 babu albashi. Mun ci bashi har abin ya wuce misali".

Gwamnatin Filato da ta gabata dai, ta ce dama ta na tantance ma'aikatan jihar ne, tantancewar da bata kammala ba, har wa'adinta ya kare.

To sai dai kuma gwamnatin ta yanzu da aka rantsara a watan Mayun da ya gabata, ta sha nanata cewa daga gwamnatin da ta gabata ta gaji wannan matasala ta ma'aiakata musamman batun albashi, kuma tana bakin kokarinta domin ganin an warware matsalar.

Ko baya ga matsalar malaman makarantun Firamare musamman masu koyar da darusan addinai, da ke bin bashin watanni goma sha takwas, su ma sauran ma'akata a jihar ta Filato na bin bashin albashi na watanni kalilan.