Bunkasa cinikin fina finan Hausa tsakanin Nigeria da Niger

Image caption Shugaban tace fina finai ta jihar Kano

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano da ke Najeriya ta ce shirye-shirye sun yi nisa tsakanin ta da gwamnatin Jamhuriyar Nijar wajen cinikayyar fina-finai a tsakani kasashen biyu.

Shugaban hukumar, Alhaji Sama'ila Na Abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa a karakashin shirin, fina finan da hukumar ta amince da su ne kadai za a rika sayarwa a Jamhuriyar Nijar.

Ya kara da cewa gwammnatain Nijar ta yi haka ne domin inganta kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma karfafa aikin da hukumar tace fina-finan take yi na samar da fina-finai masu inganci --wadanda kuma suka dace da koyarwa ta addini da tarbiya.

Wannan shiri ya samu goyon bayan ma'aikatar kasuwanci da ciniki da ma'aikatar watsa labarai ta jihar Kano da hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya da kuma hukumar kula da shirya fina-finai ta Jamhuriyar Nijar.