Bam ya hallaka mutane 19 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru sun maida hankali wajen yakar Boko Haram

Mutane a kalla 19 sun rasu sannan wasu fiye da 100 sun ji raunuka sakamakon fashewar bama-bamai a lardin arewa mai nisa a Kamaru.

Bayanai sun ce bam din farko ya tashi ne a kusa da sansanin jami'an tsaro, a yayinda daya bam din ya fashe a kusa da kasuwar kauyen Kerawa.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan kunar bakin wake ne suka kai hari a kauyen da ke kusa da kan iyaka da Nigeria.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan Boko Haram na barna a wurare

Ko a cikin watan Fabarairun bana ma sai da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari a kusa da kasuwar, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

Ana zargin mayakan Boko Haram ne ke kai hare-hare a garuruwan da ke Lardin arewa mai nisa a Kamaru musamman na garin Maroua a watan Yuli inda mutane da dama suka hallaka.

A yanzu haka dai kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin sun kafa rundunar hadin gwiwa domin murkushe 'yan Boko Haram.