ICPC: Ana binciken wasu tsofaffin gwamnoni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi na daga cikin wadanda ICPC ke tuhuma

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC, ta fara bincike a kan wasu tsoffin gwamnonin kasar guda hudu da ake zargi da almundahana da dukiyar gwamnati, sakamakon wata takardar korafi da aka rubuta a kansu.

Tsofaffin gwamnonin sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da na jihar Rivers Rotimi Amaechi da na Enugu Sullivan Chime da kuma Ibrahim Shema na Katsina.

Tuni dai aka tashi tawagogi guda hudu zuwa jihohin domin su bincika kundin ajiye bayanai na jihohin don tabbatar da gaskiyar zargin da ake wa gwamnonin.

Hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya dai sun zage dantse wajen gurfanar da duk wanda ake zargi da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya dare karagar mulki.