Nigeria ta dawo da sojoji 3,000 bakin aiki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nigeria ta sha alwashin kawar da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dawo da sojojinta 3,000 bakin aikinsu, wadanda ta kora bisa zargin da aka yi musu a baya na rashin da'a a lokacin yaki da kungiyar 'yan Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanar Sani Usman Kukah-Sheka, ya ce sun mayar da sojoji 3,032 ne daga cikin dakaru 5,000 da aka dauki matakin ladabtarwa a kansu.

Kanar Sheka ya kara da cewa "Sojojin wadanda aka mayar bakin aikinsu sun ce a shirye su ke da su koma bakin daga domin su yaki kungiyar Boko Haram kuma a yanzu haka sun fara horo a wajen horas da sojoji da ke Kontagora a jihar Naija."

A cikin watan Disambar bara ne wata kotun soji ta yanke wa wasu dakaru su 54 hukunci kisa bisa kin bin umurnin zuwa filin daga su yaki Boko Haram.

An kuma yanke wa wasu sojojin 12 hukuncin kisa a watan Satumbar bara, sakamakon bore da suka yi a Maiduguri har ma suka harbi motar kwamandansu.