Tallace tallace da ke da illa a Match.com

Image caption Match.com ya shawarci jama'a da su inganta matakan tsaro a Internet.

An gano wa su tallace tallacen wadanda ke da illa a shafin soyayya wato Match.com na Burtaniya.

Wadannan tallace tallacen dai an saka su ne a shafin inda aka yi amfani da wasu hanyoyin kai wa ga adireshin shafukan Internet.

Hakan ya sa shafin na Match.com ya dakatar da duk wasu tallace tallace na wani dan lokaci yayin da yake gudanar da bincike.

Wani mai magana da yawun Match.com ya ce ba su samu rahoton cewa masu amfani da shafin sun fada cikin tarko irin wadannan tallacen tattacen ba.

Sai dai shafin ya shawarci jama'a da su tabbatar sun inganta matakan tsaro wajen amfani da hanyoyin Internet don kare kansu.

A karshen watan Agusta ne shafin soyayya na Plenty of Fish shi ma ya fada cikin irin wannan yanayi da Match.com ya shiga.