Boko Haram ta kusa zuwa karshe - Buratai

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai

Rundunar sojojin Najeriya ta sake jaddada cewar dakarunta za su murkushe mayakan Boko Haram cikin watanni uku, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su umarni.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai ne ya shaida wa BBC hakan a wata hira da aka yi da shi.

Manjo-Janar Buratai ya kuma ce a yanzu haka suna kara jibge sojoji a bakin daga, tare da karin kayayyakin aikin da ya ce suna kara samu domin tunkarar mayakan kungiyar.

Ya ce "Ina tabbatar da cewa sojojinmu suna kokari sosai a bakin daga don haka ina da yakinin in Allah Ya so kafin watanni ukun su cika za mu kawo karshen wannan kungiya."

Manjo-Janar Buratai ya kara da cewa duk da yake an bar shiri tun rani, a yanzu rundunar sojin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burinta.