Ebola: An killace mutane 1000 a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane sama da 11,000 ne suka mutu tunda Ebola ta barke a kasashen Saliyo da Guinea da Liberia.

An killace mutane kusan 1,000 a Saliyo bayan mutuwar wata mata sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

Killacewar ta tsawon makonni uku za ta hada da dokar hana fita a wani kauye a arewacin kasar da ke yankin Kambia.

Matar ta rasu ne a ranar Asabar da ta wuce, kwana biyar bayan an sanar da cewa kasar ta yi makonni shida babu cutar ta Ebola.

Mutane sama da 11,000 sun mutu tun da cutar ta barke a kasashen Saliyo da Guinea da Liberia.