Za a tsare shugaban Guatemala a kurkuku

Image caption An rantsar da mataimakin shugaban kasar, Alejandro Maldonado a matsayin shugaban rikon kwarya

Wani alkali a kasar Guatemala ya bada umurnin tsare shugaba Otto Perez Molina a gidan fursuna bisa zargin sa da ake yi a badakalar cin hanci da rashawa na miliyoyin daloli.

Mai shari'a Miguel Angel Galvez ya ce kotun ta na ganin yana da muhimmanci ta bada umurni na wucin gadi na tsare Mr. Otto Fernandez Perez Molina kafin a fara shari'a.

A ranar Talata ne dai 'yan Majalisun dokokin kasar suka kada kuri'ar cire masa rigar kariya daga fuskantar tuhuma, lamarin daya ba ofishin babban mai shari'a na kasar damar shigar da kara akan sa.

Ya dai sha musanta zarge zargen da ake masa.

A halin da ake ciki an rantsar da mataimakin shugaban kasar, Alejandro Maldonado a matsayin shugaban rikon kwarya gabannin zaben shugaban kasar da za'a gudanar ranar Lahadi mai zuwa.