Rundunar hadin gwiwa ta samu gudunmawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Najeriya da Chad da Kamaru da Nijar su suka kafa rundunar sojin hadin gwiwar don maganin Boko Haram a kasashen su

Hukumar zartarwa ta kungiyar kasashen tafkin Chadi ta ce ta fara samun gudumuwar abokan arziki.

Rundunar sojojin samar da zaman lafiya mai dakaru dubu 8,700 da kasashen yankin suka kafa domin yakar Boko Haram na da shalkwata a Chadi.

Sakataren hukumar, Injiniya Sanusi Imran Abdullahi ne ya tabbatar da wannan labari a hirar su da wakilin BBC.

Injinya Abdullahi ya sanar da haka ne yayin wani taron manema labarai a Yamai sakamakon ziyarar aikin da ya kai inda ya gana da shugaban kasar Alhaji Muhammadou Isufu.

Ya ce gudunmawa mafi tsoka ta fito daga Najeriya a inda Shugaba Muhammadu ya bai wa rundunar dala miliyan 100.