Sarkin Saudiyya zai ziyarci Obama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama a lokacin da ya kai ziyara Riyadh wajen sarki Salman

A ranar Juma'a ne sarkin Saudiyya Salman bn Abdul'aziz zai gana da shugaba Obama a birnin Washington, a ziyararsa ta farko zuwa Amurka tun bayan da ya dare mulki a watan Janairu.

Rahotanni sun ce kasashen biyu masu amintaka da juna suna so su gyara dangantakarsu ne da wasu al'amura suka fara shafarta.

Ana sa ran sarki Salman zai bayyana damuwar kasashen Larabawa masu arziki "Arab Gulf Countries," kan yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliya na kasar Iran.

Suna tsoron cewar dage takunkumi zai iya bai wa Iran damar kara goyon bayan kungiyoyin ta'addanci masu haddasa rikice-rikice da ake fama da su a gabas ta tsakiya.

Kazalika, ana tsammanin Amurka za ta tursasa sarkin ya sassauta wajen kai hare-haren da kasarsa ke jagoranta zuwa Yemen, domin a samu damar kai agajin gaggawa ga wadanda suke cikin bukata.