BH: Kasashen Afirka na taro a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyoyin Boko Haram da ta Alshabab su ne manyan batutuwa a taron

Manyan hafsoshin tsaron kasashen kungiyar tarayyar Afirka wato AU na taro a Bamako, babban birnin kasar Mali da nufin yaki da ta'addanci.

Babbar manufar taron dai ita ce samun hadin gwiwa tsakanin kasashen na Afirka wajen kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram a kasashen da ke kewaye da tafkin Tcadi da na kungiyar Alshabab da ke addabar kasashen Somalia da Kenya.

Mahalarta taron dai sun nanata bukatar da ke akwai na gano irin girmar matsalar ta'addanci da kuma daukar dukkannin matakan da suka dace wajen dakile shi.

Sauran abubuwan da kasashen suka mayar da kai a kai su ne dakile manyan laifuka kamar safar miyagun kwayoyi da safarar makamai da ta mutane.

Sauran matsalolin su ne na bakin haure da wariya da kuma danniya a kasashen na Afirka.

Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin na daya daga cikin wadanda ke halartan taron.