Bishop Idowu ya kama aiki

Image caption Bishop Idowu Fearon ya zama babban sakataren Cocin Anglican

Sabon babban Sakataren Cocin Anglican, Arch Bishop Idowu Fearon, ya kama aiki bayan ya sha rantsuwar fara aiki a Ingila.

Idowu Fearon dai ya kasance dan Afirka na farko da aka nada a kan wannan mukamin.

Wannan kuma yana zuwa dai-dai lokacin da ake samun sabanin ra'ayi tsakanin mabiya Cocin da ke nahiyar Afirka da takwarorinsu da ke Amurka da Turai a kan batun auren jinsi daya da kuma nada mata a matsayin Limaman addinin Kirista.

Idowu dai ya ce duk da cewa batun auren jinsi haramun ne a Najeriya amma ya ce hakan ba zai hana masu mambancin ra'ayin zaman lafiya.

Gwamnatin Najeriya ta aika tawagarta zuwa Ingila domin taya sabon babban Sakataren Cocin Anglican murna.