Amurka tana son a mutunta 'yancin sirrin mutane

Image caption Wasu hukumomi dai suna amfani da fasahar wajen kama mutane

Gwamnatin Amurka tana kara lamba kan yadda jami'an tsaro suke amfani da fasahar zamani wajen kama masu laifi.

Kamfanonin wayoyi na jabu da ake wa lakabi da Stingrays suna ba da bayanai akan mutanen da ake zargi da aikata laifuka.

Suna kuma neman bayanai akan mutanen masu wucewa wadanda ba su yi laifin baki ba ballantana fari.

Sai dai kuma yanzu haka gwamnatin Amurkar ta ce dole ne hukumomi su samu takardar da za ta ba su iznin bincike akan mutum kafin a yarje musu yin amfani da fasahar gano masu laifin.

Gwamnatin dai ta ce ta dauki wannan matakin ne da zummar martaba sirrin 'yan kasar.

Kuma dokar ta shafi hukumar bincike ta FBI, hukumar sanya ido kan shan giya da taba da kuma mallakar makamai.

Sauran hukumomin da dokar ta shafa su ne hukuma mai kula da inganci magungunan da kuma bangaren shari'a na kasar.

Image caption Wasu ma suna fake wa da fasahar don samun bayanan mutane ne

Sai dai kuma dokar ba ta shafi 'yan sandan garuruwa ba duk kuwa da cewa tuni daman wasu jihohin kasar kamar Washington da Virginia da Minnesota da kuma Utah suka sanya dokar samar da takardar neman iznin binciken wadanda ake zargi da aikata laifi.