'Karbe makamai ne maganin rigima a arewa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar ta ce akwai makamai a hannun mutane

Wata kungiyar 'yan arewacin Nigeria da ke zaune a kudancin kasar ta Northern Nigeria Unity Congress, ta ce matakan da gwamnatin Buhari ya kamata ta dauka wajen dakile rikice-rikicen addini da kabilanci a arewacin kasar shi ne na kwace makamai daga hannun mutane.

Kungiyar ta ce mutane da dama a birane da kauyuka suna rike da makamai a yankin sabanin yadda aka sani a baya.

Kungiyar ta Northern Nigeria Unity Congress ta kuma yaba da matakan da gwamnatin ta dauka kawo yanzu wadanda kungiyar ta ce sun inganta zamantakewa tsakanin kabilu a kasar.

Rikice-rikicen addini da kabilanci sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane sannan sun tilasta dubbai barin gidajensu a yankin na arewacin Najeriya.