Kamaru ta tisa keyar 'yan Nigeria 1,000

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan gudun hijrar da aka dawo da su sun fi 1000

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta ce ta karbi mutane sama da 1000 tsakanin ranakun Asabar da Lahadi wadanda hukumomin kasar Kamaru suka dawo da su zuwa Najeriya.

'yan gudun hijrar wadanda mafi yawancinsu mata ne da kananan yara na daga cikin wadanda da ke neman mafaka a Kamaru bayan rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin gidajensu.

Yanzu haka, hukumar ta NEMA ta sauki 'yan gudun hijrar a sansanoni guda uku da ke jihar Adamawa kafin daga bisani a kai su garuruwansu idan da bukatar hakan.

Babban jami'in hukumar a Yola, Bello Sa'ad ya ce wasu da dama daga cikin 'yan gudun hijrar sun zo a galabaice sakamakon cunkosan mota.

Ko a makonni biyu da suka gabata ma hukumar ta NEMA ta karbi 'yan gudun hijrar fiye da 6000.