An rufe majami'u a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An rufe majami'un ne saboda damun mutane da suke yi

Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas ta ci tara tare da rufe majami'u sama da 55 a fadin jihar saboda damun jama'a da suke yi.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamkon yadda mutane ke kokawa bisa yadda wuraren ibadar ke amfani da amsa kuwa na wuce makadi da rawa.

Hukumar ta kare muhalli ta ce ta ba wa coci-cocin umarnin rage sautin amsakuwwarsu amma su ka ki bin umarnin.

Hukumar dai ta ce sai majami'un sun rattaba hannu akan yarjejeniyar cewa za su dai na damun mutane kafin a sake bude wuraren ibadun.