"Burtaniya za ta iya shiga kaka-ni-kayi"

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Archbishop Justin Welby

Archbishop na Canterbury, Justin Welby ya yi gargadin cewa Birtaniya za ta iya shiga halin kaka-nakayi idan majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin da zai ba wa marasa lafiya dake gab da mutuwa damar karisa kansu.

Archbishop Welby ya yi gargadin ne a jaridar 'The Observer' inda ya ce shi da wasu shugabannin addini a Birtaniya sun rubuta wa 'yan majalisar dangane da batun.

Ya ce sun ja hankalin 'yan majalisar cewa ka da su kuskura su rattaba hannu a kan kudurin da zai ba mutane marasa lafiya ikon kashe kansu.

Archbishop Welby ya ce idan aka rattaba hannu a kan kudurin dokar, likitoci za su samu damar ba marasa lafiya maganin kashe kansu wadanda suka nemi su mutu kuma aka tabbatar ba za su rayu fiye da watanni shida ba.