Mutane 14 sun hallaka a hadarin kwale kwale

Hakkin mallakar hoto AP

Hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar yara mata goma sha hudu, inda sha daya suka rasu a kogin Sarkin Pawa, uku suka nutse a kogin Guni.

Kifewar kwale kwalen dai ya tada hankali al'ummar yankin dama gwamnatin jihar baki daya.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar Neja Dr ibrahim Dooba ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA reshen jihar Neja Garba Salihu yace suna daukar matakan kare aukuwar irin wannan hadrin a nan gaba da kuma taimakawa iyalan mutanen da hadarin ya ritsa da su.