Saudiyya za ta tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarki Salma na Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya ta na shirin rage kudaden da ta ke kashewa saboda tasirin faduwar farashin mai, wanda shi ne babban jigon gudanar da gwamnatin kasar.

Ministan kudi, Ibrahim Alassaf yace, wasu manyan ayuka da tuni aka amince da yinsu, yanzu za a dakatar da su.

Duk da cewa bai bada cikakken bayani akan wuraren da tsuke bakin aljihun zai shafa ba, amma yace, lamarin ba zai shafi bangaren kiwon lafiya, da ilimi ba.

Hukumomin Saudiyya sun yi hasashen cewa, zasu fuskanci gibin dala biliyan arba'in a kasafin kudin bana, amma masana sun ce, gibin ya wuce haka nesa ba kusa ba.