BBC: Za a bude sashe saboda 'yan Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Hall ya ce za a tsage gaskiya komai dacinta

BBC na shirin kaddamar da sashe mai watsa shirye-shirye domin 'yan Habasha da kuma Eritrea a matsakaici da kuma gajeren zango a rediyo, in ji Darekta Janar Tony Hall.

A jawabinsa, Mr Hall ya bayyana shirin soma watsa wasu shirye-shirye ga wasu yankunan duniya da ke fama da "gibi na siyasa a kan labarai masu tsage gaskiya."

"Wannan tsarin zai bude wata kofa ga BBC domin wanzar da mulkin demokradiyya," in ji Hall.

A yanzu haka dai BBC na watsa shirye-shirye ga Afrika a harsunan Ingilishi da Faransanci da Kinyarwanda da Hausa da Somali da kuma Swahili.