BH: Sojojinmu suna kokari sosai - Buhari

Image caption Hirar BBC ta farko ga wata kafa bayan cika kwanaki 100 a kan mulki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya ce jami'an tsaron kasarsa sun samu nasara matuka a yaki da kungiyar Boko Haram.

A hirarsa da Editan sashen Hausa na BBC, Mansur Liman, shugaba Buhari ya ce akwai bukatar a kara matsa kaimi wajen kawo karshen 'yan kunar bakin wake wadanda ke ci gaba da kaddamar da hare-hare.

Buhari ya ce idan aka yi la'akari da kudaden da aka bai wa jami'an tsaro, a ganinsa sun yi abin a yaba wajen murkushe 'yan Boko Haram.

"Burinmu shi ne mu hana su kwace kauyuka da garuruwa amma kuma sai an dauki lokaci mai tsawo kafin a hana su kai harin kunar bakin wake," in ji Buhari.

Tun lokacin da aka rantsar da Shugaba Buhari a watan Mayu, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane fiye da 1,000.

A kan batun cin hanci da rashawa, Buhari ya ce yana hada kai da kasashen duniya domin kwato kudaden da aka sace musamman na danyen mai da ake sacewa a cikin teku.