Shugaba Buhari zai kai ziyara Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai wata ziyarar wuni daya a kasar Ghana.

Shugaba Buharin zai sauka a birnin Accra ne tare da mai bashi shawara kan harakokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da kuma manyan jami'an ma'aikatar tsaron Najeriya.

Sauran sun hada da jami'an ma'aikatar harkokin waje da masana'antu da kuma cinikayya.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama, da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar ne zasu tarbi shugaban na Najeriya.

Shugabannin biyu tare da jami'an su zasu tattauna batutuwan tsaro a yammacin Afrika da kuma sha'anin kasuwanci tsakanin Najeriya da Ghana.

Shugaba Buhari zai gana da wasu 'yan Najeriya mazauna Ghana kafin ya koma kasar sa.