Jamus za ta taimakawa 'yan hijira

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan gudun hijira a Jamus

Gwamnatin Jamus ta sanar da wasu jerin matakai na taimakawa kasar yin dawainiya da tururuwar 'yan gudun hijira da ta samu.

Matakan sun hada da samar da karin kudi dala biliyan 3 domin taimakawa jihohi da kuma gundumomi.

Sauran matakan sun hada da saukaka hanyoyin samun izinin mafaka ga 'yan hijiran, da samar musu matsugunnai da kuma samar da kudi na dawainiya da sabbin 'yan hijirar da zasu shiga kasar.

Gwamnatin ta sanar da matakan ne bayan wata ganawa ta sa'o'i 5 tsakanin shugaba Angela Merkel da kuma wasu shugabannin kasashen Turan masu kuduri irin nata.

Akalla 'yan hijira dubu 18 ne aka yi kiyasin sun shiga Jamus a ranakun karshen mako bayan wata yarjejeniya da aka cimma da Austia da Hungary game da sassauta ka'idojin neman izinin mafaka.