Za a ci gaba da shari'ar Habre a Dakar

Hissene Habre Hakkin mallakar hoto
Image caption Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre

A ranar Litinin za'a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre, a Dakar babban birnin kasar Senegal.

Ana tuhumar Mista Habre da bayar da umurni a kisan da aka yi wa mutane 40,000 a zamanin mulkinsa a shekarun 1980.

Ana kuma tuhumar Mista Habre da azabtarwa da kuma aikata miyagun laifuka a kan bil adam.

A watan Yuli ne aka dage shari’ar da ake yi masa bayan da Mista Habren ya bayyana kotun a matsayin haramtaciyya kuma ya umurci lauyoyinsa a kan kada su halarci zaman kotun.

Idan ya ki amincewa da sabbin lauyoyin da aka nada domin su kare shi, watakila alkalin kotu ya yanke shawara a kan ko kotun za ta ci gaba da sauraron karar.