An dauki mataki kan manyan motoci a Lagos

Image caption Manyan motoci na janyo cunkoso a Lagos

Gwamnatin jihar Lagos da ke kudancin Nigeria ta kafa dokar haramta wa manyan motoci zirga-zirga a kan hanyoyin jihar da rana.

Dokar za ta fara aiki ne daga karfe shidda na safe zuwa tara na dare a kowacce rana.

Gwmanatin jihar Lagos ta ce wannan mataki ya zama dole domin rage cunkoso da kuma afkuwar haddura da ake zargin manyan motocin na haddasawa.

Sai dai masu manyan motocin sun ce ba hakan batun yake ba.

Ana yawan samun haddura a kan hanyoyi a Nigeria musamman da manyan motoci abin da ya janyo mutuwar mutane da dama.