Boko Haram: An haramta hawa dawaki

Shehun Borno ya ba da hadin kai

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shehun Borno ya ba da hadin kai

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya na cewa, sojojin kasar sun haramta amfani da dawaki da jakuna a kauyukan da ke jihar.

Bayanai sun ce an dauki matakin ne saboda yadda a baya-bayan nan mayakan kungiyar boko Haram suka fito da wani sabon salo na kai hare-hare a kan dawakai.

Wani mai sarautar gargajiya a jihar Borno ya shaida wa BBC cewa, Shehun Borno ne da kansa ya shaida musu wannan doka kuma za su bayar da goyon baya 100 bisa 100

Kazalika bayanai sun nuna cewa rundunar ta dauki matakin hana cin kasuwannin kauye inda nan ne ma 'yan Boko Haram suka fi kai hare-harensu, da kuma kwace kayayyakin abinci da na masarufi.

Wadannan na daga cikin matakan da sojojin Nigeria suka dauki domin kawo karshen ayyukan 'yan Boko Haram.