NNPC ya soma aikin dawo da dala biliyan 7

Ibe Ikachikwu Hakkin mallakar hoto NNPC
Image caption Shugaban kamfanin mai na NNPC Ibe Ikachikwu

Kamfanim man fetur a Najeriya NNPC ya ce ya fara aikin dawo da wasu makudan kudade da suka haura dala biliyan 7 da ya biya a matsayin haraji.

Kamfanin ya ce harajin da ya biya ya wuce ka'ida a kan wasu manyan ayyukansa.

Cikin wani rahoto da ya gabatar wa shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kamfanin NNPC, Mista Ibe Kachikwu ya ce sun dukufa wajen tabbatar da matatun man kasar sun ci gaba da aiki yadda ya kamata kafin karshen wannan shekarar.

Tun bayan da aka nada shi a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPC Mr Kachikwu ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa a bangaren man fetur din Najeriya.