An fara gangamin neman zabe a Myanmar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jagorar 'yan adawa a Myanmar Ms Aung San Suu Kyi

An fara gangamin yakin neman zabe a Myanmar, watanni biyu kafin zaben shugaban kasar na farko da jama'a zasu iya tsayawa takara a cikin shekaru 25.

Jam'iyyar National League for Democracy-NLD wadda Aung San Suu Kyi da ta taba shan dauri saboda banbanci ra'ayi na siyasa ke jagoranta, zata kara da jam'iyyar mai mulki Union Solidarity and Development wadda sojoji ke marawa baya.

Ms Suu Kyi a wani faifan bidiyo, ta bayyana zaben da za a yi a watan Nuwamba a matsayin mai muhimmanci wanda zai kawo sauye sauye na zahiri da ake bukata.

Sai dai kuma, kundin tsarin mulkin kasar ya dakatar da Ms Suu Kyi daga zama shugabar kasar koda kuwa jam'iyyar ta ce ta samu kuri'u mafi yawa a zaben.

Zaben shi ne zai zamo na farko tun da aka kafa gwamnatin far hula a 2011, sai dai ganin yadda har yanzu sojoji ke da karfin iko a kasar, da dama na zargin mai yiwuwa zaben ba zai zamo na gaskiya ba.