An dakile harin bam a Nairobi

Image caption Al-Shabab na yawan kai hari a Kenya

An kama mutane uku a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da wani mutum ya yi kokarin shiga wani rukunin kantina dauke da bama-bamai.

Masu gadin wajen ne suka ci karfinsa, sannan 'yan sanda suka lalata bama-baman.

An yi amannar wani dan karamin bam ne mai batir da wata wayar salula manne a jikinsa, wanda da shi ne zai yi amfani da shi a matsayin kunamar bam din.

Tuni aka kwashe mutanan da ke cikin rukunin shagunan na Garden City.

Shekaru biyu da suke wuce,kimanin mutane sittin da bakwai aka kashe lokacin da aka masu tayar da kayar baya na kungiyar Al-Shabab suka kai hari rukunin shaguna na Westgate da ke Nairobi.