Fasfo: An dirar ma tsofaffin gwamnoni

Image caption Hukumar NIS ta ce za ta dauki mataki a filayen jiragen sama

Hukumomi a Nigeria za su kwace fasfo na diplomasiyya da kuma na jami'ai daga hannun tsofaffin jami'an gwamnati.

Hukumar kula da shige-da-fice ta kasar, NIS ce a cikin wata sanarwa ta bayyana haka inda ta ce matakin ya shafi tsofaffin gwamnoni da sanatoci da ministoci da wasu mutanen da suka taba rike manyan mukamai a gwamnati.

Sanarwar daga shugaban hukumar, Martin Abeshi ta ce duk wanda ya ki bin wannan umurnin za a dauki mataki a kan sa a filin jirgin sama.

"Kin bin wannan umurnin ya saba wa dokar 'Immigration Act 2015'. Kuma za a dauki mataki kan wadanda suka karya dokar," in ji Abeshi.

Sanarwar ta bukaci duk wadanda suke rike da fasfo na diplomasiyya su mayar wa hukumar a ofishinta na Abuja.