Fafaroma zai gyara tsarin saki da kome

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fafaroman yana san gyara tsarin saki da kome ne ba canja koyarwar darikar ba

A ranar Talata ne ake sa ran Paparoma Francis zai sanar da sabon tsarin da mabiya darikar Katolika za su bi wajen sakin mata da kuma sake aurensu.

A bara ne dai Fafaroman ya kafa wani kwamiti mai kunshe da lauyoyin cocin da zummar yin nazari kan tsarin.

Ana yi wa tsarin saki da kome lakabi da rushewa ko kuma annulment.

Idan dai ba a rushe dokar da ta hana sakin da sake aure ba to yin saki da kome ka iya zama zina abin da kuma zai haramta wa ma'aurata zaman aure.

Sai dai kuma fafaroman ba wai zai canja koyarwar darikar ta Katolika ba ne dangane da saki, illa iyaka dai ya nemi ya sassautawa ma'auratan da suka rabu amma kuma suna kaunar juna.