Mutanen da ke mutuwa daga saran maciji za su karu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maciji

Kungiyar agaji ta likitoci Medicines San Frontieres ta yi gargadin cewa za a iya samun karuwa ta yawan mutanen da suke mutuwa sakamakon saran maciji yayin da ake fuskantar karancin maganin saran macijin.

Kiyasi ya nuna cewa mutane 100,000 suke mutuwa a kowacce shekara sakamakon saran maciji kuma kashi biyu bisa uku daga cikinsu, suna yankin kudu da sahara ne.

Kungiyar ta MSF ta ce maganin saran maciji da ya yi tasiri sosai a yanki wanda ake kira Fav-afrique zai kare a tsakiyar shekarar 2016.

Kamfanin da ke samar da magani na kasar Faransa ya daina samar da maganin a bara saboda, a cewarsa, ba ya samun ciniki wajen sayar da maganin.