An samu raguwar mutuwar kananan yara

Image caption Unicef da WHO sun ce akwai sauran jan aiki

Wani rahoto na hukumar lafiya ta duniya, WHO ya ce an samu raguwa da kashi 50 cikin 100 na mutuwar kananan yara tun daga shekarar 1990.

Rahoton wanda WHO tare da hadin gwiwar Unicef suka fitar, ya nuna cewar shekaru 25 da suka wuce yara 'yan kasa da shekaru biyar su kusan miliyan 13 ne suka rasu.

Amma kuma a bana, alkaluma sun nuna cewa yara kasa da miliyan shida ne suka rasu.

Sai dai a cewar WHO da Unicef har yanzu akwai babban kalubale kan batun.

Bayanai sun ce duk da raguwar da aka samu, amma ba a cimma burin da majalisar dinkin duniya ta yi kokarin cim masa ba.