Mayaka na tafka ta'asa a Darfur

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe dubban mutane a rikicin Darfur

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce dakarun da gwamnatin Sudan ke goyan baya na ta kashe-kashe a yankin Darfur.

A wani rahoto, kungiyar ta ce sojojin sakai da ake kira dakarun ba da tallafin gaggawa ko kuma 'Rapid Support Forces', sun yi ta yin lalata da mutane da kona gidaje da kuma lalata rijiyoyi.

Wani da ya shaida abin da ya faru, ya ce dakarun sakai sun yi wa mata 17 fyade a wani asibiti.

Kungiyar kare hakkin bil-adama din ta soki dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Darfur a kan rashin yin wani abin azo a gani na kare fararen hula.