An kama 'yan Boko Haram da kwayoyi

Miyagun kwayoyin da rundunar sojin Najeriya ta capke
Image caption Miyagun kwayoyin da rundunar sojin Najeriya ta capke

Runduna ta Uku ta Sojin Najeriya da ke jihar Borno ta ce ta kama wasu mutane da miyagun kwayoyoyi da kuma tabar wiwi a cikin wata mota a garin Geidam na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

Rundunar ta yi zargin cewa mutanen ne ke kai wa mayakan kungiyar Boko Haram man fetur da miyagun kwayoyi irin su wiwi da madarar Suck and die da kuma Tramol.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani Kukasheka Usman, ya ce sojoji sun kama mutanen ne a wurin binciken abubuwan hawa a hanyar Depchi zuwa Geidam.

Ya ce sun yi nasarar kama mutanen ne bayan umarnin da hedikwatar tsaro ta bayar ga sojoji a kan su kara kaimi wajen binciken abubuwan hawa a yankin arewa maso gabashin kasar.