Boko Haram: Sojoji sun sako mutane 128

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption An mika wadanda aka sako ne a ga gwamnan jihar a wani biki a Maiduguri

Rundunar sojin Nigeria ta sako wasu mutane 128 da take tsare da su wadanda ake zargin mayakan Boko Haram ne.

Babban hafsan mayakan kasa na kasar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ne ya mika mutanen a wani dan karamin biki a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Mutanen da aka sako sun hada da maza 109 da mata bakwai da kuma kananan yara maza su 11.

A waje daya kuma rundunar ta ce barnar da mayakan Boko Haram suka yi a garin Gamboru Ngala ta wuce misali.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa babu ko da tsuntsu a garin sai dai jami'an soji da ke sintiri.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty

Bayanai sun ce an kafa tutar Najeriya a garin na Gamborou, sannan dakarun Nigeria sun karasa kan iyakar kasar da Kamaru inda mutanen yankin suka fito suna yi wa dakarun maraba.