Apple ya kaddamar da sabbin wayoyi

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin Apple ya kaddamar da wata kwamfutar iPad mai girma da 'TV box' da kuma sabbin wayoyin iPhones da za su iya gane yadda ake latsa s.

Kamfanin ya nuna cewa an kirkiri iPad Pro domin a yi wasannin bidiyo da kallon fina-finai da kuma tace hotuna.

Cinikin kwamfutocin iPad da kamfanin ya kirkiro tun da farko na fuskantar ja da baya.

Kwamfutar ta iPad Pro na da inchi 12.9.

Apple ya sayar da kashi 19% na kwamfutocin iPads tsakanin farkon watan Oktoba da kuma karshen watan Yuni kamar yadda ya yi a daidai wannan lokacin shekara guda da ta gabata.